8 Agusta 2021 - 19:57
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Ya Yaba Wa Kasashen Larabawan Da Suka Kulla Alaka Da Isra’ila

Faisal Bin Farhan ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da wasu kasashen larabawa suka yi da cewa hakan yana da kyau.

ABNA24 : Shafin yada labarai na Shehab News ya bayar da rahoton cewa, Faisal Bin Farhan ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana, kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da gwamnatocin UAE, Bahrain, Sudan da kuma Morocco suka yi, zai taimaka wajen samun ci gaba a yankin.

Ya ce a lokacin da aka gudanar da zama a yankin Al'ula na Saudiyya an samu fahimtar juna a tsakanin Saudiyya da Qatar, bayan kwashe tsawon shekaru suna zaman doya da manja.

Kafin wannan lokacin dai matsayar Saudiyya ita ce ba za ta amince da kulla alaka ta zahiri da Isra'ila ba, matukar ba a kafa kasar Falastinu a akan iyakokin shekara ta 1967 ba, wanda kuma sabon furucin ministan harkokin wajen kasar ya yi hannun riga da wannan matsaya.

Gwamnatocin kasashen UAE da Bahrain gami da Sudan da Morocco, sun kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila bisa matsin lamba daga gwamnatin Trump, yayin da kuma wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suka ki mika wuya ga wannan matsin lamba na Amurka, duk kuwa da cewa wasu gwamnatocin Larabawa suna da mu’amala da gwamnatin yahudawan Isra’ila tsawon shekarua cikin sirri.

342/